Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al’waay News cewa, bisa la’akari da yawan hare-haren maratani da kungiyar Ansarullah ke kaiwa kan garin Jizan mahukuntan kasar Saudiyyah na shirin kulla wani makirci na yunkurin kashe Sheikh Nimr ta hanyar kai shi gidan kaso na Jizan, ta yadda za su kashe shi, sai dora alhakin hakan kan Ansarullah da harin da suke kaiwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan makirci na mahukuntan wahabiyawan Saudiyyan ya tonu bayan da wasu suka habarta hakan ga wasu bangarori, wanda kuma daga karshe labarin ya fito fili kowa ya san da hakan, bayan da aka watsa shi a kafofin yada zumunta.
Mahukuntan Saudiyya sun kame shekh Nimr ne sakamakon irin matakan da ya dauka na kalu balantar zaluncin masarautar wahabiyawan Saudiya, da kuma irin mummunan bakin mulki na zalnci da danniya da take yi kan al’ummar kasar.
Shehin malamin dai yan azaune a yankunan gabacin kasar wanda mafi yawansu mabiya mazhabar shi’a ne wadanda gwammnatin wahabiya ta kasar ke nuna musu banbanci matuka a cikin dukkanin lamurra da suka shafi ‘yan kasar, duk kuwa da cewa dukkanin arzikin danyen mai da isa gas da kasar ta dogara da shi ana fitar da shi ne daga wannan yanki nasu.
Har yanzu dai mahukuntan masarautar Al-saud bas u yanke shawara guda daya ba kan yadda za su kashe Sheikh Nimr wanda ya zame musu kadangaren bakin tulu.
Tun bayan kame shi sun fara kai shi gidan Kason Dammam da ke gabacin kasar, kafin daga bisani suka dauke shi zwa gidan Kason Riyadh.
3360096