IQNA

Mutane 107 NE Suka Rayukansu Wasu 238 Suka Samu Raunuka A Masallacin Harami

21:46 - September 12, 2015
Lambar Labari: 3361731
Bangaren kasa da kasa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fadowar na'urar daga kayan aiki a haramin Ka'abah mai tsarki ya kai 107, yayin da wasu kimanin 238 suka samu raunuka.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Saudi Gazette cewa, Sulaiman Amr mai kula da ayyukan agajin gaggawa y ace isak mai tsanani ne ya haifar da wannan matsala.

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a haramin Makkah sun haura zuwa 107 sakamakon fadowar karfen da ke lodin kayayyakin gine-gine a jiya Juma’a.

Mahukuntan Saudiyya a safiyar yau Asabar sun sanar da cewa; Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fadowar karfen da ke lodin kayayyakin gine-gine a kan rufin haramin Makkah sun haura zuwa 107 tare da jikkatan wasu fiye da 240 na daban.

Majiyar watsa labaran Saudiyya ta sanar da cewar sakamakon ruwan sama da matsananciyar iska da ke kadawa a birnin Makkah a jiya Juma’a sun yi sanadiyyar gurbatar yana yi tare da karya bishiyoyi gami da fadowar dogon karfen da ke lodin manyan kayayyakin gine-gine a kan rufin haramin Makkah lamarin da ya yi sanadiyyar rubzawarsa a kan mutane da suke gudanar da ayyukan ibadu a cikin haramin.

Kuma ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane fiye da dari da aka dauke da motocin ambulance 39 akalla tare da jikkatan wasu fiye da na daban da suka hada da maniyata aikin hajjin bana da suka fito daga wasu sassan duniya.

3361475

Abubuwan Da Ya Shafa: makka
captcha