Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin shugaban kasa cewa, matain sakon shugaban kasa kamar haka:
Da Sunan Allah mai rahma Mai Jin Kai
(Farko daki da aka saka ma mutane shi ne wanda yake a Makka mai albarka kuma shiya ga talikai)
Rasa rayukan da alhazai suka yi a kasa mai tsarki da suka hada har da alhazai Iraniyawa, hakika wannan abu ne mai sosa zuciya da saka damuwa da bakin ciki matuka.
Wanann lamari ya faru ne a cikin kwanaki da ake gudanar da aikin hajji a daki mai alfarma tare da halartarv musulmi dag akoina cikin fadin duniya, wanda hakan abin bakin ciki ne, kuma muna isar da sakon taya bakin ciki ga wadanda abin ya shafa baki daya.
Shugaban kasar Iran ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a cikin masallacin Harami mai tsarki a Makka, tare yin addu'ar Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu, haka nan kuma ya bayyana cewa Iran a shirye take ta karbi dukkanin wadanda suka samu raunuka domin yi musu magani.
Hassan Rauhani shugaban kasar Iran
3361608