IQNA

Jami’ar Azhar Ta Kori Dalibanta 300 Saboda Dangantakarsu da Kungiyar Daesh

21:54 - September 13, 2015
Lambar Labari: 3362167
Bangaren kasa da kasa, wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa jami’ar Azahar ta masar ta korar dalibanta har kimanin 300 da suka da dangantaka da kungiyar yan ta’adda ta Daesh.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, bayan samunb bayanai jami’ar ta Azahar ta haramtawa wa wadannan dalibanta dari uku ci gaba da karatu a karkashinta.

Bayanai sun tabbatar da cewa kungiyar Daesh tana kokarin hada wata kungiya ta daliban kasashen ketare da suke da karatu a Azahar domin gudanar da wasu ayyuka na ta’addanci da wani suna na daban.

Wasu daga cikin yan kungiyar yan uwa musulmi ne suke daukar nauyin tattara daliban kasashen ketare da ke karatu aa jami’ar Azhar, tare da saka su kanhanya ta yan ta’addan Daesh, ta hanyar tura su zuwa kasar Turkiya daga can kma sais u hade da yan kungiyar.

Jami’ar Azhar ta bukaci dukkanin sauran rassanta da ke cikin kasar da su zama cikin fadaka dangane da daliban kasashen ketare, tare da kuma sanya ido a kansu da kuma dukkanin harkokinsu, domin tabbatar da dewa yan ta’adda ba su samu ktsawa a cikinsu ba.

Masu karatu a jami’ar dag suke zuwa daga kasashen ketare su ne suka fi saurin ruduwa da batun shiga kungiyoyin yan ta’adda, inda sukan zama a sahun gaba a cikin kungiyoyin yan ta’adda masu tayar da fitina.

3361838

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha