IQNA

Jami’an Jordan Sun Yi Allawadai Da Kai Harin sahyuniyawa Kan Masallacin Aqsa

23:49 - September 14, 2015
Lambar Labari: 3362569
Bangaren kasa da kasa, jami’an gwamnatin kasar Jordan sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin aqsa mai alfama.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Petra cewa, Muhammad Mumini ministan yada labarai a kasar Jordan ya bayyana shirin Isra’ila na mamaye quds da cewa ya saba wa dokokin kasashen duniya.



Ita ma a nata bangaren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi Allawadai da ke alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan sahyuniya suke yi a birnin Quds da ma sauran yankunan Palastinu, gami da cin zarafin palastinawa marassa kariya.

Babban jami’in mai kula da harkokin Palastinu a cikin kungiyar hadin kan kasashen larabawa ne ya sanar da hakan a jiya a babban ofishin kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya ce kungiyar tana nuna takaicinta matuka dangane da yadda yahudawan sahyuniya suke ta tsananta ayyuknsu na cin zarafin Palastinawa.

Haka na kuma kakakin gwamnatin Jordan yace Isra’ila ta yi watsi da tattaunawar da suka a 2014 tare da Sarki Abdullh kan batun birnin Quds, shi ma mai kula da harkokin palastinu ya ce kungiyar za ta ci gaba da bin dukkanin hanyoyi da suka dace domin kalubalantar gwamnatin yahudawan Isra’ila da nufin taka mata birki kan wannan ta’asa.

A nata bangaren kungiyar kasashen musulmi ta ce za ta gudanar da wani zama nan ba da jimawa ba  akasar Morocco, domin yin dubi kan abubuwan da suke faruwa a palastinu, musamamn a birnin Quds.

Fiye da mutane dari ne suka samu raunuka sakamakon farmakin da yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin Quds mai alfarma a jiya Lahadi, tare da yin awon gaba da wasu fiye da ashirin.



3362272

Abubuwan Da Ya Shafa: jordan
captcha