IQNA

Jami’ain Tsaron Sahyuniyawa Sun Karya Kofar Alkibla Ta Masallacin Quds

22:28 - September 15, 2015
Lambar Labari: 3362966
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun karya kofar alkibla ta masallacin Quds mai alfarma a ciki gaba da kai farmakin da suke yi kan masallacin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na kafofin yada labaran Palastinu cewa, mutane 17 daga masu baiwa masallacin kariya sun jikkata sakamakon dauki ba dadin da suka yi da yahudawan.

Kwanaki uku a jere yahudawa masu tsatsauran ra’ayi da kuma jami’an tsaro haramtacciyar kasar suke ci gaba da kaddamar da farmaki kan masallata  acikin wannan masallaci tun daga ranar asabar, inda fiye da mutane dari  ne suka samu raunuka sakamakon farmakin da yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin Quds mai alfarma a jiya Lahadi, tare da yin awon gaba da wasu fiye da ashirin.



Wasu rahotanni daga birnin Quds sun ce yahudawa masu tsatsauran ra’ayi ne suka kai harin tare da daruruwan ‘yan sanda Isra’ila a cikin kayan sarki da suke ba su kariya, ‘yan sandan Isra’ila sun shiga cikin masallacin, inda lakada wa masallata duka, tare da tarwatsa su da barkonon tsohuwa, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane fiye da dari daya.



Baya ga fitar da masallata tare da lakada musu duka, yahudawan sun banka wuta a wasu sassa na masallaci, inda ska kama da wuta har wasu suka kone a ynkurinsu na neman kashe wannan wuta, amma duk da haka kasashen larabawa suna ci gaba da yin gm da baknansu kan wannan ta’asa.



3362846

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha