IQNA

An Gano Kwafin Kur’ani Guda Dubu 70 Masu Nakasu A Kasar Saudiyyah

23:54 - September 21, 2015
Lambar Labari: 3365995
Bangaren kasa da kasa, daga farkon fara ayyukan hajjin bana an gano kwafin kur’ani mai tsarki kimanin dubu 70 masu nakasua cikin kasar Saudiyyah.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa, jami’an tsaron kasar sun tsayar da wata bababr mota dauke da kwafin kur’ani mai tsarki kimanin dubu 70 da suke da kure wajen bugunsu ana shirin raba su ga mahajjata a Makka.

An cafke wadannan kur’anai ne da aka bug aba bisa kaida ba, wadanda wasu cibiyoyin wahabiya suke bugawa suna rabawa a matsayin ayyukan alkhairi ga jama’a da suke gudanar da ayyukan ibadar haji a kasar, wanda hakan ya sanya za a gudanar da bicike kan lamarin.

Bayan cafke mutanen, an kuma tattara dukkanin kwafi-kwafi na dukkanin kur’anan an mika su ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar, wadda za ta gudanar da nata binciken kan lamarin, daga bisani kuma ta sanar da matakin da za a dauka kan duk wadanda suke da hannun a cikin wanann barna.

A karshen watan da ya gabata ma mahkuntan na Saudiyya sun kame wasu kwafin kur’ani mai tsarki guda 5600 da aka buga su da nakasu kuma ake shirin raba su ga musulmi.

Jmi’an tsaron sun ce mutmin da yake tuka motar da take dauke da kur’anan balarabe dan wata kasa da yake aiki a kasar, kuma an kama shi ana gdanar da bincike kansa, daga bisani kuma za a mika shi zuwa kotu, inda a can ne za a kammala dukkanin bincike kan dukkanin wadanda suke da hannun cikin lamarin.

3365618

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha