IQNA

‘Yan salafiyya Na Hankoron Jawo hankulan ‘Yan Gdun Hijira Musulmi

12:27 - September 24, 2015
Lambar Labari: 3366974
Bangaren kasa da kasa, wata cibiya a kasar jamus ta bayar da wani bayani da ke nuni da cewa yan salafiyya suna ta hankoron jawo hankulan musulmi daga cikin masu gudun hijira a turai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Jamus cewa, bisa ga wani rahoto da ta hada yan salafiyya masu tsatsauran ra’ayi suna ta hankoron jawo hankulan musulmi daga cikin masu gudun hijira a kasar.

Wannan cibiyar ta kasa a Jamus ta bayar da wannan rahoton ne da ke cewa yanzu haka wahabiyawa masu dauke da mmmunar akidar nan ta kafirta musulmi sun fara farautar wasu daga cikin musulmi masu gudun hijira a Monikch.

Rahoton ya ce wadanann wahabiyawa suna kokarin kara fada ayyukans tun bayan da ‘yan gudun hijirar suka fara fantsama a cikin kasashen turai, inda suke yin amfani da makudan kudade domin wanke kwakwalen wasu daga cikinsu domin mayar da su kan tafark\insu na tsatsauran ra’ayi.

Sau tari dai wannan cibiya ta yi gargadin cewa ya zama wajibi kan mahukuntan kasar da su dauki matakan hana yaduwa ayyukan kungiyoyin wahabiya yan salafiya, domin kuwa su ne amsu tallar akidar ta’addanci kuma hakan yana tatatre da hadari ga kasar da ke gabacin turai.

Akidar kafirta musulmi ta wahabiya da kuma salafawa na daga cikin abubuwa masu matukar hadari da gwamnatocin kasashen turai suke tsoron yaduwarsua  halin yanzua  cikin kasashensu, bayan da suka fahimci cewa ba dukkanin musulmi ne yan ta’adda ba, wadanda suke dauke da wanann akida nea ake samun yan ta’adda a cikinsu.

3366161

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha