IQNA

23:38 - September 24, 2015
Lambar Labari: 3367099
Bangare siyasa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa an kafa wani kwamiti domin bin kadun alhazan kasar Iran da suka rasu a hadarin Minna a yau.


Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya habarta cewa Amir Hussain Abdullahiyan mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, tun har an kafa wani kwamiti domin bin kadun alhazan kasar Iran da suka rasu a yau a hadarin Minna mai sosa rai.

Yace abin da ya faru yau mai sosa rai ne matuka, kuma ya zama wajibi mahukuntan kasar Saudiyya su yi bayani kan hakikanin abin da yake faruwa, tare da yin bayani kan sakacinsu.

Y ace suna bin kadun lamarin yadda ya kamata domin tabbatar da adadin maniyyata Iraniyawa da sukia rasu a hadarin na yau, kamar yadda kuma suke bin kadun lamarin tare da wakilin Wilayar Faqih a can.

3367002

Abubuwan Da Ya Shafa: Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: