Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na PressTV cewa, bayan watsa labarah da wasu kafofin yada labarai suka yi kan mutuwar tsohon jakadan Iran a kasar Lebanon Ghazamfar Rukn Abadi a Mina, dan uwansa na jinni Morteza Rukn Abadi ya bayyana cewa, tun jiya Juma’a ba su samu wani bayani danagne da makomarsa ba, amma dai suna ci gaba da bincike.
Ya ce tun jiya suna ta buga wayarsa ta salula amma dai har yanzu ba su samu wani bayani ba, domin ba a daukar wayar tasa.
Morteza Rukn Abadi ya karyata rahotannin da ke cewa dan uwansa ya rasu a abin da ya faru jiya a Mina, inda ya ce babu wani dalili da ke tabbatar da cewa dan uwansa ya rasu, amma dai suna cikin bin kadun lamarin domin samun cikakken bayani a kan makomarsa.
Kafin wannan lokacin jaridar Al-diyar ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, Ghazamfar Rukn Abadi ya rasu jiya a lokacin da aka samu tirmitsitsin a lokacin jifar shaidan a Mina, amma babu wani dalili da ke tabbatar da wannan rahoto na jaridar.
3368222