IQNA

Mai Magana Da Yawun Ma’aikatar Harkokin Waje Ta Yi Allawadai Da Harin San’a

18:11 - September 25, 2015
Lambar Labari: 3369330
Bangaren kasa da kasa, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addanci da aka jiya a wani masallaci a birnin San’a na kasar Yemen.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa Mardiyyah Afkham mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane harin ta’addancin da aka kai jiya a wani masallaci birnin San’a a lokacin sallar idi.

A lokacin da take bayanin, mai Magana da yawun ‘aikatar harkokin wajen ta bayyana cewa, irin wadannan ayyuka na ta’addanci suna kara fitowa da hakikanin fuskar wadanda suke aikata hakan da cewa makiya dukkanin al’ummar kasar Yemen ne.

Dangane da kai harin a ranar salla kuwa, ta ce yan ta’adda ba su da addini balanata su girmama kimar wani addini ko wasu lamurra masu kima a cikinsa, a kan haka babu banbanci a wurinsu a kowane lokaci za su iya aikata hakan kan al’ummar msuulmi.

Ta kara da cewa al’ummar yamen suna cikin wani yanayi na balain da aka jefa sua  ciki, sakamakon harin wuce gina da irin da ake kai wa kansu ta sama da kasa, da kuma na ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan wadanda ke kai harin ta sama.

Kan haka ta ce ya zama wajibi a kai taimakon gagawa ga al’ummar Yemen na abinci da magunguna da sauran abbuewan bukatar rayuwa, kamar yadda kuma ya zama wajibi masu kashe al’ummar Yemen ta sama da kasa su dakatar da hakan.

3367081

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha