Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hamrain News cewa, Ayatollah Ozma Ali Sistani bababn marja’i na kasar Iraki ya yi kira da a dauki matakan gaggawa domin kada a sake samun matsalar da aka samu Mina a wannan shekara.
Babban malamin ya bayyana abin da ya faru a Mina da cewa babban abin bakin cikin ne mai sosai rai matuka, kuma wajibi a kan dukkanin kasashen musulmi su dauki matakan da suka dace domin ganin an kawo karshen faruwar hakan a nan gaba.
Ayatollah Sistani ya ce yana mika sakon ta’aiyya ga iyalan wadanda wannan lamari ya rutsa da su, wadanda suka rasa rayukansu Allah ya jikansu ya gabatar musu, wadanda kuma suka jikkata yana rokon ubangiji ya ba su lafiya.
Daga karshen bayanin nasa Ayatollah Sistani ya kara jadda muhimmancin daukar lamarin hajji da matukar muhimmanci, kuma wajibi ne da ya rataya kan kasashen msuulmi baki daya, da kuma wadanda usuke da hannu wajen gudanar da wannan lamari.
Wannan babban hadari da ya faru a Mina dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 1300, yayin da wasu fiye da 2000 suka jikkata, kamar yadda kuma wasu kimanin 136 daga cikin mahajjatan kasar Iran suka rasa rayukansu.
3370571