Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, a jiya bangaren kur’ani na cibiyar Imam Hussain (AS) ya fitar da bayani da ke isar da sakon ta’aziyya dangane da shahadar biyu daga cikin fitattun makaranta kur’ani mai tsarki na kasar Iran a Mina a ranar jifar shaidan.
Bayanin ya ce Darul qur’an na cibiyar Hussaini tana isar da sakon ta’aziyya a cikin bakin ciki dangane da shahadar fitattn makaranta kr’ani mai tsarki na kasar Iran Mohsen Haji Hassani Kargar da kuma Muhammad Bawi, wadanmda suka yi shahada a kasa mai tsarki.
Bayanin ya ce wadannan bayin Allah biyu Iraniyawa makaranta sun karba kiran ubangiji ne a lokacin da suke aikin ibada a filin Mina.
Bayanin na Darul qur’an ya ce; muna rokon Allah da ya jikan wadannan bayi nasa, ya sada su gafararsa kuma ya baiwa iyalansu hakurin rashinsu, tare da sauran masoyansu a duk inda suke.
3372758