Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a jaridar Al-riyad cewa, Khalid Faleh da kuma Hasan Hashemi ministocin harkokin lafiya na Iran da Saudiyya sun tattauna kan batun dauko gawawwakin kasar da dawo da su.
Adadin alhazan kasar Iran da suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru a Mina a lokacin jifar Shaidan ya kai mutane 464, yayin da kuma wasu suke kwance a asibiti suna jinya.
Hukumar alhazai ta kasar Iran ce ta sanar da hakan a yau a cikin wani bayani da ta fitar, inda ta ce bayan gudanar da bincike a dukkanin asibito da aka ajiye gawawwakin alhazan kasar a Saudiyya da kuma wadanda suka samu raunuka, a yau an kammala tantace adadin mahajjatan kasar da suka rasu sakamakon abin da ya faru a Mina, wanda ya kai 464.
Kasashe da dama sun nuna rashin jin dadin dangane da rashin samun cikakken bayani daga mahkuntan Saudiyya kan hakikanin adadin alhazansu da suka rasa rayukansa da kuma wadanda ba a ji duriyarsu ba.
Ana ci gaba da yin Allawadai da da yadda mahukuntan saudiyya suke ci gaba da kin bayyana bayanai kana bin da ya faru ga gwamnatocin kasashen da suka rasa alhazansu a abin da ya faru.
3377002