IQNA

Wasu Daga Cikin Dangin Alhazan Kasar Moroco Na Shirin Kai Kai Saudiyya kara

18:50 - October 06, 2015
Lambar Labari: 3382529
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin dangi da iyalan wasu alhazai na kasar Moroco da suka rasu ko suka bata na shirin shigar da kara kan mahukuntan Saudiyya.

//Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya natal to daga shafin sadarwa na yanar gizo na Morocco World News cewa, yanzu haka wasu daga cikin dangi da iyalan wasu alhazai na kasar Moroco da suka rasu ko suka bata sakamakon abin da ya faru a Mina na shirin shigar da kara kan mahukuntan Saudiyya kan rashin sanin makomar danginsu.

 

Shi ma a nasa bangaren shugaban tawagar mahajjatan kasar Morocco kuma ministan tattalin arzikin kasar Muhammad Bu-Sa’eed ya koka kan yadda jami’an gwamnatin kasar Saudia suke mu’amala da jami’an kiwon lafiya na sauran kasashen musulmi  kan bin ya faru a Minaa  hajin ba.

Jami’in  yana cewa jami’an gwamnatin kasar Saudia sun ki amincewa jami’an kiwon lafiya na kasar Morocco su isa wararen ajiye gawawwaki don gano mutanen kasar da aka rasasu bayan hatsarin na Mina.

 

Baynai sun ce alhazan kasar ta Morocco 19 ne suka rasu, wasu kimanin 37 kuma suka bata bat  tun bayan aukuwan wannan hatsarin an daukesu cikin wadanda suka rasu ne kawai.

Sarki Muhammad na shida ya aike da ministan kiwon lafiya na kasar zuwa Saudiyya domin bin kadun makomar alhazan kasar da suka rasu da kuma wadanda suka bat, duk kuwa da cewa har yanz akwai bayan da ke cewa an rufe wasu daga cikin alhazan ba tare da an tantance sub a.

 

http://www.iqna.ir/fa/News/3382293

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha