Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Batra cewa, Ahmad Tayyib Sheikhul Azhar a lokacin ganawarsa da sarkin Abdullah na biy na Jordan ya bayyana cewa duk da matsalolin da ake fama da su a duniyar yau amma masallacin Aqsa na cikin zukatan musulmi biliyan daya da rabi na duniya.
Sojin Haramcecciyar kasar Isra’ila na ci gaba da kai harin kan Al’ummar Palastinu, a safiyar yau Sojojin haramtacciyar kasar yahudawa sun yi halbi kan masu zanga-zanga a garin baitul Il dake arewacin amalla, lamarin da yayi sanadiyar shahadar wani Matasi guda, sannan kuma sun yi awan gaba da masu zanga-zangar da dama.
Har ila yau a yau din dai Sojojin na ISra’ila sun halbe wata matashiya har lahira a kofar babul majlis dake gabashin Baitu-makdis, sannan kuma a safiyar ta yau Sojojin na haramtacciyar kasar yahudawa sun budewa yahudawa masu tsatsauren ra’ayi kofar masallacin Qudus, inda suka keta alfarmarsa
A cikin ‘yan kwanakin nan dai Sojojin na haramtacciyar kasar yahudawa na yawan kai hari kan masallata a masalacin na Qudus, a wani shiri da suke kokarin aiwatarwa na raba lokutan Ibada tsakanin Al’ummar musulmi da yahudawa a masallacin Qudus mai alfarma.
Ahmad Tayyib ya ce yana da matukar muhimmanci muuslmi su zama cikin fadaka damgane da abin da yake faruwa akan yan uwansu, haka nan kuma ya yi ishara da kokarin da ake yi shawo kan samari masu fadawa a cikin kungiyoyi da ayyuka na ta’addanci a duniya.