Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, a jiya darurwan matasa a birnin Ribat na Morocco sun gudanar da gangami domin nuna rashincewa da abin da ya faru na kisan mahajjata a Mina a lokacin aikin hajjin bana wanda shi ne mafi muni a tarihin hajjin a musulnci.
Shi ma a nasa bangaren wani likitan kasar Masar ya yi zargin cewa an fesawa mahajjata iska mai guba ce a Mina Kafar watsa labarun al-mudih, ta Saudiyya ta buga cewa wanda likita ne dan kasar Masar, kuma jami’i na ma’aikatar kiwon lafiyar Saudiyya, ya rbutawa sarkin Saudiyya wasika da aciki ya yi zargin cewa an yi amfani da guba akan mahajjata.
Wannan likitan ya ci gaba da cewa baya da ya bincika gawawwaki masu yawa da su ka fadi a Mina, sannan kuma da ganin wasu da su ka tsira, ya kai ga cimma matsaya cewar an yi amfani da iska mai guba.
A can kasar Masar ma likitoci da dama sun bayyana cewa mutanen da su ka jkkata wadanda aka kai su asibiti, sun kamu da cutar manutuwa.
Dubban mahajjata ne dai da su ka fito daga kasashe daban-daban na duniya su ka rasa rayukansu, bayan toshe wata daga cikin hanyoyi da aka yi a wurin jifar shaidan.
3383083