Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na news-alwaled.com cewa, Abbas shoman mataimakin bababn malamin Azhar ya bayyana a cikin wani kira da ya yi da sunan cibiyar cewa, ya kamata a kafa wani kwamiti na kasashen msuuolmi da rika tsara ayyukan hajji da Umarah a kowace shekara domin kauce ma irin abin da ya faru a bana.
Ya ci gab ada cewa bisa la’akari da cewa wannan aiki na ibada ya shafi dukkanin al’ummar musulmi ne ba wani bangare ba, to ya zama a saka kowane bangare na muslmi domin su bayar da tasu gudunmawar domin tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai.
Abubuwan da suka faru a wannan shekara dai sun saka ayar tamabaya kan yadda masarautar gidan Saud take tafiyar da lamurran aikin haji, musamman ganin yadda aka kashe mutane da dama daga cikin mahajjata a wanann shekara, sakamakon rufe wa mahajjata kofofin wucewa a mina a lokacin jifa.
Kasashen duniya da dama sun yi na’am da irin wadannan shawarwari na neman a mayar da tsarin wannan aiki a hannun dukkanin kasashen musulmi ta hanyar kafa kwamiti da hada su baki daya tare da yin aiki na bai daya.
Tuni dai sarkin masarautar ta iyalan gidan Saud ya ki amincewa da irin wadannan shawarwari, inda yake ganin cewa su ne kadai suka dace da hakan, domin kuwa su ne masu mulki a kasar kuma su ne suka fi kowa sani ya kamata a yi.