Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tena cewa, a cikin wadannan kwanaki cibiyar muslunci ta Imam Hussain (AS) za ta dauki nauyin shirya tarukan juyayin tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a babban ginin cibiyar da ke da sunansa.
Wannan taro an riga an fara shit un jiya tare da halartar malamai, inda Shekh Hassan Al-amiri daya daga cikin malaman kasar Iraki ya gabatar da jawabi ga maharkata wannan wuri a cikin harshen larabaci, sheikh Ali Akbar sadiq kuma ya gabatar da nasa acikin turanci, sai kuma Sayyd Haidar Alawami ya yi bege.
A kowace shekara ana gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura da kuma Arbain, inda ake gabatar da jawabai da suka shafi ranar, inda ake samun halartar mutane na kasashen Iraki, Syria, Lebanon, Iran da kuma Afghanistan.
3385806