IQNA

An Yi Kira Da A Dauki Kwararan Matakan Kare Masallacin Aqsa

23:07 - October 17, 2015
Lambar Labari: 3386753
Bangaren kasa da kas, mahalarta taron nuna goyon bayan ga masallacin Aqsa a Turkiya sun yi kira da dauki matakan gaggawa wajen kare masallacin mai alfarma daga mamayar sahyuniyawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, mahalarta taron nuna goyon bayan ga masallacin Aqsa a Turkiya sun yi kira da dauki matakan gaggawa wajen kare masallacin Aqsa daga ta’addancin yahudawa.

A bangare guda kuma ani bayawude dan kama guri zauna a yankin Palastinu ya bindige wani matashi Palastine a safiyar yau Assabar Matashin mai suna Mufid Sharbani an bindige shi ne a anguwar Alkhalil kuma shekarunsa ba su fice 14 ba, bayan shahadar wannan matashi, adadin Palastinawan da suka yi shahada cikin makuni biyu ya haura zuwa arbain.

Kafafen watsa Labarai sun habarta cewa ana ci gaba da gumurzu tsakanin Palastinawa da Dakarun tsaro haramcecciyar kasar Isra'ila a yankuna daban-daban dake kan iyakar kasar da kasar Jodan.

A jiya juma'a ma Palastinawa biyar  ne suka yi shahada sanadiyar halbin da Sojojin HKI suka yi musu a lokacin da suke zanga-zanga a yankunan zirin gaza da kuma kan iyakar kasar da jodan.



Kungiyar bada Agajin gaggawa ta Palastinu ta bayyana cewa daga farkon watan oktoba zuwa yanzu kimanin Palastinawa 50 suka ji munanan rauni bayan mutanan da suka yi shahada sakamakon farmakin da Sojojin HKI ke kai musu.



3386425

Abubuwan Da Ya Shafa: aqsa
captcha