IQNA

‘Yan Shi’a Masar Suna Gudanar Da Juyayin Shahadar Imam Hussaini A Cikin Gidajensu

21:58 - October 18, 2015
Lambar Labari: 3388695
Bangaren kasa da kasa, masani dan kasar Masar kuma mabiyin tafarkin Ahlul bait (AS) a kasar Masar mamba ababbar cibiyar Ahlul bai ta duniya ya bayyana cewa sna gudanar juyayin shahadar Imam Hussain (AS) ne a cikin gidajensu.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na ynar gizo na jaridar Yaou Sabe cewa, Taher Alhashemi masani dan kasar Masar kuma mabiyin tafarkin Ahlul bait (AS) a kasar Masar ya sheda cewa mabiya mazhabar shi’a  akasar ta Masar, tun daga farkon Muharram har zuwa Arbain suna gudanar juyayin shahadar Imam Hussain (AS) ne a cikin gidajensu na kansu, amma daga lokcin sai tafi ziyara wurin Ra’as Hussain (AS) da ke birnin Alkahira.

Wannan masani ya ci gaba da cewa, babu wata hujja da wani zai fakewa da ita wajen karyata a bin da ya faru da Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon Allah a hannun azzaluman sarakunan lokacinsa, domin kuwa hatta wadanda suke kokarin yin musun wannan lamari a cikin kasar, ayyana wani wuri da sunan cewa a  nan a ka a jiye kan Imam Hussain (AS) bayan shahadarsa, ya isa ya zama dalili na karyata su.

Baya ga haka kuma y ace akwai hadisan ma’aiki (SAW) masu tarin yawa wadanda dukkanin bangarori sun ruwaito su, daga ciki kuwa har da hadisin da manzo ke cewa ni daga Hussain nake, Hussaini kuma daga gare ni yake, wanda hakan kadai ya isa ya zama dalili da take tabbatar da matsayin Imam Hussain (AS)

Dangane da yadda ake gudanar da irin wadannan taruka na Ashura masu albarka, ya bayyana cewa akwai banbanci tsakanin kasashe da kuma al’ummomi, bisa la’akari da banbanbcin mahanga tsakanin musulmi kan yadda suke kallon lamarin.

Taher Alhashemi y ace a kasar Masar suna gudanar da tarukans tsawon shekaru ta hanyar da yanayi ya basu a kasar, inda sukan karanta kur’ani da kuma karanta musibar da ta afka kan Imam Hussain (AS) da saurn iyalan gidan manzo tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

3387047

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha