Kamfanin dillanicin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, wanann horo za a gudanar da shi ne bisa take gogewa a fagen kur’ani kuma nan da ‘yan kwanaki za a gudanar da shi a masallacin juma’a na Azhar.
Wannan horo zai kunshi koyar da hardar kur’ani mai tsarki, kwarewa wajen karatun tilawa, kyautata sautin karatun kur’ani, da kuma koyar ilmomin kira’a daban-daban da suke a cikin tsarin karatun kur’ani.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannin taro na bayr da horo kan kur’ani zai gudana ne karkashin kulawar Muhammad Mahna daya daga cikin masu kula da masallacin Azhar, sai kuma Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar ta Azhar.
3387106