IQNA

UNESCO Ta Yi Allawadai Da Isra’ila / Tel Aviv: UNESCO Ta Zama Bangaren Rikici

17:04 - October 22, 2015
Lambar Labari: 3391732
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da adana kayan tarihi ta majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya kana bin da Isra’ila take na sace kayan tarhi lamarin da ya fusata jami’an yahudawa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, UNESCO ta amince da wani daftrin kudiri da aka gabatar da ke yin kakkausar da yin Allahawadai kan rusa wuraren tarihi da kuma sace wasu muhimman kayan tarihi, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya.

Wannan kuwa ya hada da yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take kaddamar da hari kan yankuna da kuma yadda take rusa duk wani abu na tarihi a cikin birnin quds da sauran yankunan palstinawa, d ahakan ya hada har masallacin Aqsa mai alfam da ke fuskantar irin wadannan ayyukan na dabbanci daga Isra’ila.

Kasashen Kuwait, Masar, UAE, da Tunisia gami da Algeriya ne suka gabatar da daftarin kudirin, inda kasashe 26 suka amince da shi daga cikin kasashe 58 mambobin hukumar.

Kasashe 25 daga cikin mambobin bas u ce komai ba, yayin da 6 da suka hada da Amurka, Birtaniya, Jamus, Holland, Czech da kuma Autonia suka ki amincewa da hakan sam, bayan da suka hau kujerar naki tare da nuna cikakken goyon bayansu kan wannan ta’asa da Isra’ila take aikatawa da ta sabawa dkkanin dokoki.

Tun kafin wannan lokacin dai an saba gabatar da kudurori a hukumomi na kasa da kasa domin taka wa Isra’ila birki kan ta’addancinta  akan al’ummar palstinu da ma sauran al’ummomi na yankin, amma wadannan kasashe suna nuna rashin amincewarsu.

Masallacin Aqsa na daga cikin muhimman wurare na mabiya addinin muslunci da ke fuskantar tozarci a hannun yahudawan Isra’ila, amma kasashen duniya musamman na musulmi sun yi gum da bakunansu.

3391651

Abubuwan Da Ya Shafa: unesco
captcha