Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Hamrain News cewa, ma’aikatar kula da harkokin naddini a kasar Masar wato ta bada umurnin rufa masallacin Imam Husain da ke birnin Alkahiri a dai dai lokacinda mabiya mazahabar Ahlulbaiti (a) a kasar suke juyayin Tasu’a da Ashoora a yau Jumma’a da gobe Asabar.
Rahotannin sun ce ma’aikatar ta bada umurnin rufe masallacin ne a jiya da dare, sannan ta yi barazanar daukar mataki a kan duk wanda ya bude shi har zuwa karshen juyayin Ashoora.
Shugaban kungiyar yan Shia a birnin Alkahiri Ahmad Rasim Annafis ya yi kakkausar suka da Allah wadai kan matakin da ma’aikatar addinin ta dauka na rufe masallacin.
Annafis ya kuma kara da cewa wannan yana nuna cewa akwai wasu masu fada a ji cikin ma’aikatar wadanda suke da ra’ayin wahhabiyanci masu gaba da yan shia.
Irin wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wadannan matakai da ake dauka kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ba a kasar ta Masar, domin kuwa da dama daga cikin gwamnatocin da akyi a baya-bayan nan musamamn sun dauki irin wanann mataki na rashin adalci ba.
Shi dai masallacin Hussain (AS) dai yana daga cikin wurare da mabiya tafarin shi'a suke ziyarta a ranakun tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a cikin kwanaki muharram da ake raya su domin tunawa da shahadarsa da kuma sadaukrwarsa a lokacin waki’ar.
Akwai mabiya tafarkin iyalan gidan manzoa koina suna raya wadannan ranaku nab akin ciki da tunawa da musibar da ta samu iyalna gidan manzo a lokacin da suke ta tare da Imam Hussain (AS) a cikin wadannan ranaku na wanann wata da a ke juyayi.
3392818