Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Ruusia Today cewa, hare-haren da aka kai a yankunan arewa maso gabacin Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 55. Tare da jikkatar wasu fie da 100.
Hukumomi a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane 27 ne suka mutu a harin bam din da aka kai a birnin Yola, kakakin gwamnatin jihar ya shaida cewa mutane 96 ne suka samu raunuka.
Wadansu da suka shaida lamarin sun ce an tayar da bam din ne a Masallacin Jambutu da ke Jimeta a dai-dai lokacin da ake tayar da Sallar Juma'a.
A can Maiduguri babban birnin Jihar Borno mutane na ci gaba da zaman jimami bayan wasu hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 28 tare da jikatar wasu da dama.
3393040