IQNA

Warware Matsaloli Ta Hanyar Tattaunawa Shi Kadai Mafita

22:16 - October 28, 2015
Lambar Labari: 3407232
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Iran Hojjatol Islam Rouhani a lokacin da yake ganawa da sabon jakadan kasar Sudan ya bayyana cewa warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna shi kadai ne mafita da za ta kawo karshen tashin hanklai a yankin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ha barta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shugaban kasa cewa, a jiya shugaban kasar Iran Hojjatol Islam Rouhani a lokacin da yake ganawa da Adel Ibrahim Mostafa sabon jakadan kasar Sudan a Iran ya bayyana cewa warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna shi kadai ne mafita da za ta kawo karshen tashin hanklai a yankin da ma duniya baki daya.
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya bayyana cewa warware matsalolin da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna ya fi alkhairi ga kowa, maimakon haddasa yake-yake da zubar da jinni.
Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake karbar takardun sabon jakdan kasar Sudan a Iran Adel Ibrahim Mustafa, inda ya ce yana kira ga dukkanin bangarori na kasashen yankin da ma sauran kawayensu larabawa da su zabi hanyar tattaunawa da sulhu wajen warware matsalolin da ake fama da su a cikin wasu kasashen yanki, musamman Yemen, maimakon lugudan wuta a kan al’ummomin wannan kasa maras kariya.
Sheikh Rauhani ya kara da cewa a shekarun da suka gabata, Iran da Sudan sun kace a sahun gaba wajen taka wa ‘yan mulkin mallaka birki a yankin, kuma yana fatan Sudan za ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a kasashen larabawa.
A nasa bangaren sabon jakadan na kasar Sudan a jamhuriyar muslunci t Iran Adel Ibrahim Mustafa ya bayyana cewa, kasarsa na goyon bayan Iran a tattanawar da kasashen 1+5 da Iran, hakan an kuma  a kowane lokaci za su kasance a matsayin kasashe masu kyakyawar alaka  adukkanin bangarori, a matsayi na kasa da kada da kuma yankin.

 

3398239

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha