Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, kungiyoyin masu rajin kare hakkinbil adama a taron manema labarai da suka yi a birnin San’a, sun zargi Saudiyya da yin amfani da makaman da aka haramta a duniya a kan al’ummar kasar Yemen a harin da suke kaiwa kansu.
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa, soki kasar Saudiyya saboda harin da jiragen yakinta su ka kai wa wani asibiti a kasar Yemen, inda a jiya laraba ne dai kungiyar kare hakkin bil’adaman ta kasa da kasa ta bayyana cewa; Harin da jiragen yakin Saudiyyar su ka kai wa asibitin kungiyar likitoci ta duniya a garin Sa’adah na Yemen, laifin yaki ne, kuma wajibi ne a gudanar da bincike akai.
Bayanin ya ci gaba da cewa; Hare-haren babu kakkautawa da Saudiyyar ta ke kai wa yana tabbatar da cewa cikin ganganci ta kai wa asibitin na Sa’adha hari.
Wani sashe na bayanin kungiyar ya ce; Wannan ba shi ne karon farko ba da jiragen yakin Saudiyyar su ka kai wa asibiti hari, don haka dole ne a dauki matakin kare fararen hula.
A ranar lahadin da ta gabata ne dai, jiragen yakin Saudiyyar su ka kkai hari akan asibitin kungiyar, kamar yadda kuma aka tabbatar da cewa makaman da aka haramta tun 2008, an yi amfani da su wajen kaddamar da hare-haren.
3427130