IQNA

Babban Mai bayar da Fatawa A Masar Ya Bukare Musulmin Kasar Faransa

22:37 - November 14, 2015
Lambar Labari: 3449517
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa a kasar shuki Allam ya bukaci mahukuntan kasar Faransa da su kare rayukan muslmin kasar Faransa dangane da matakin da wasu ak iya dauka a kansu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum sabi cewa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa abin da ya faru na harin ta’addanci a Paris ka iya jawo hare-hare kan musulmin kasar ,a a kan haka bukaci mahukuntan kasar Faransa da su kare rayukan muslmin kasar Faransa da su da wani laifi kan wannan abu.
Shi ma a nasa bangaren daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkokin musulmi da sauran bakin da suke zaune a kasar Faransa ya bayyana damuwarsa dangane da yiyuwar bullar siyasar cutar da musulmin kasar Faransan da takura musu biyo bayan harin da aka kai birnin Paris a daren jiya Juma’a.
Kafafen dillancin labarani ya nakalto cewa daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkokin musulmin da sauran baki yana bayyana damuwarsa dangane da yiyuwar fara takurawa musulmi da cutar da su saboda wannan harin da aka kai, ya kara da cewa ‘yan kungiyar ta su sun nuna damuwarsu ainun dangane da wannan hari na ta’addanci da ya faru, to amma duk da haka ya bayyana damuwar kan yiyuwar cutar da musulmi.
Gwamnatin kasar Faransan dai ta bayyana cewar za ta dau matakan nuna rashin sani ko sabo wajen mayar da martani ga wannan harin, lamarin da ke kara sanya tsoro dangane da irin matakan da za ta dauka kan musulmin kasar .

 

Jerin hare-haren ta’adancin da aka kai da yammacin jiya juma’a a Paris babban birnin Faransa su ne mafi muni a cikin tarihin kasar tun bayan shekara ta dubu da dari tara da arba’in da biyar kawo yanzu dai mutane sama da dari da ashin.
3447857

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha