IQNA

Yaki Da Hadarin Ta’addanci Aiki Ne Na Dukkanin Al’ummomin Duniya

22:40 - November 14, 2015
Lambar Labari: 3449518
Bangaren siyasa, shugaban jamhuriyar muslunci ta Iran ya aike da sakon taya ta’aziyya ga al’ummar kasar Lebanon dangane da harin ta’addanci da aka kai a birnin Beirut.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shugaban kasa cewa, Hojjatol Islam Hassan Rauhani ya aike da sakon kamar haka:

Da Sunan Allah mai rahma Mai Jin kai

Al’ummar kasar Lebanon

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah wa Barakatuhu

Daga bangaren al’ummar kasar Iran mutanen kasar Lebanon masu hakuri masu gwagwarmaya muna isar da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da al’ummar kasa gami da gwamnati baki daya.

Abin da ya faru ya kara tabbatar da cewa ayyukan ta’addanci da kuma wadanda suke dauke da wanann mummanr akida babbar barazana ga al’ummomin yankin da ma na duniya baki daya,a  kan haka ya zama wajibi a kan dniya tamike domin yaki da su.

Daga karshe ina rokon Allah da ya gafarta ma wadanda suka rasu, ya bayar da lafiya ga wadanda suka jikkata, ya kuma iwa al’ummar kasar Lebanon baki daya hakuri.

Hassan Rauhani

Shugaban Jamhuriyar Muslunci ta Iran

3447995

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha