Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, Ahmad Tayyib babban malamin Azahar ya yi kakkausar suka tare da nuna bacin ransa dangane da danganta kungiyar Daesh da kafafen yadda labarai suke yi da addinin muslunci domin bata sunansa.
Ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya kasashen turai su dira a kan musulmi da kuma addinin muslunci sakamakon kai hare-haren birnin Paris, kuwa su sun fi kowa sanin su wanen wadannan yan ta’adda, kamar yadda kuma sun san sauran musulmi da yadda suke kallon wannan kungiya.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan kungiya ta yan ta’adda ta cutar da kowa ba tare da bambabci tsakanin musulmi da wand aba musulmi ba, bil hasali ma wadanda suka fi cutuwa daga ayyukan wannan kungiya musulmi.
Ahmad Tayyib ya ce ya kamat gwamnatocin kasashen turai su ja hankulan kafofin yada labaransu danagne da yada kiyayya kan addinin muslunci sakamakon abin da ya faru na harin ta’addanci, domin kuwa wannan lamari ya hada har da su kansu a musulmi a kasar Faransa.
Daga karshe ya yi da a hada karfi da karfe a tsakanin dukaknin kasashen duniya wajen tunkarar wannan lamari, domin tabbatar da cewa an dakushe karfin wadannan yan ta’adda da kuma wadanda suke daukar nauyinsu domin gudanar da wadannan ayyukan na ta’addanci da suna muslunci.
3453117