IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai Da Kan Hare-Hare A kan Masallatan Musulmi A Turai

19:51 - November 17, 2015
Lambar Labari: 3453885
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azahar ta yi Allawadai da akkausar murya dangane da harin da wasu suke kaiwa kan musulmi da masallatai a cikin kasashen turai.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, cibiyar Azahar ta yi Allawadai da akkausar murya kan yadda gwamnatocin wasu kasashen turai suke bari ana kai hari kan musulmi da masallatai a cikin kasashensu.

Bayanin ya ci gaba da cewa irin matakan da wasu shugabannin gwamnatoci an nahiyar turai suke dauka na danganta abin da ya faru na harin ta’addanci a Paris da kuma addinin muslunci, hakan ya karfafa gwiwar wasu masu kyamar Musulunci wajen kai hare-hare a kan musulmi.

Wajabcin Yaki Da Tunanin daesh

Abbas Shoman mataimakin babban alamin cibiyar Azahar ya bayyana cewa, wajibi ne a mike a yaki kungiyar Daesh ba tare da kakkautawa ba har sai an ga bayansu baki daya.

Ya ce abin da wannan kungiya take yi bas hi da wata alaka da addinin muslunci, kuma yin hakan shi ne bababna bin da ke bayar da dama ga masu kyamar muslunci su ci karensu babu babbaka a kan musulmi da suke zaune a cikin kasashen nahiyar tirai.

3453601

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha