Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Press TV cewa, bisa ga rahoton gkididdiga da majalaisar dinkin duniya ta bayar, ya zuwa daga farkon shekara kungiyar yan ta’addan Boko Haram ta rusa adadin makarantu da ya kai dubu daya da 100 a kasashen yankin tabkin Chadi.
Toby Lanzer wani jami’in majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa; wadannan makarantun suna a cikin kasashen Najeriya, Nijar da Chadi ne.
Ya kara da cewa kimanin mutane miliyan 2.6 ne suka bar gidajensu a wadannan kasashen domin tsira da rayukansu, kimanin miliyan 2.2 daga cikin mutanen Najeriya ne.
Kuma tun daga cikin shekarar 2009 ne kungiyar ta fara rushe makarantu da kai musu hare-hare.
A cikin shekarar bana kadai kungiyar bokoharam ta rushe makamrantun da su ka haura dubu daya.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel, Toby Lanzer yana fadin cewa; Daga farkon wannan shekara ta zuwa yanzu kadai, kungiyar ta Bokoharam ta rusa makarantun da su ka kai adadin dubu daya.
Wannan adadin a cikin kasashen Kamaru da Chadi da Najeriya da Nijar ne Lanzer ya ci gaba da cewa kasashen da asarar rusa makarantun da Bokoharam su ka yi, ya fi shafa sune Kamaru da Chad da Nijeriya da Nijar. Ita dai kungiyar ta Bokoharam tana adawa ne da tsarin karatun boko.
3453607