Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar France 24 cewa, Abbas Shoman mataimakin babban malamin Azahar ya bayyana cewa, cibiyar a shirye take ta tura masu tunatarwa da wa’azi zuwa kasar Faransa domin kalubalantar masu dauke da akidun tsatsauran ra’ayi.
Shiman ya kara da cewa Azhar din tana shirye ne ta tura wasu masu tnatarwa har zuwa daga cikin kasashen turai domin rusa akidun da masu kafirta musulmi suke yadawa na ta’addanci a kasashen.
Ya ce bayan da Daesh ta sanar da cewa it ace ke da alhakin harin da aka kaia Paris ya zama wajibi a dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar wannan babban hadari.
Abbas Shoman ya ce tun kafin kai harin Paris sun bayar da shawara ga Faransa a matsayin Azahar bababr cibiyar musulunci ta duniya kan Fransa ta bari su aike da malamai zuwa sassa na kasar domin wayar da kan musulmi kan tatsaran ra’ayi da kuma akidar ta’addanci da ake cusa musu.
Shoman ya kara da cewa a halin yanzu ba su da wasu muhimman ayyuka da suke gudanarwa na addini a cikin Farasa da ma sauran kasashen turai, wanda kuma hakan babban kure, wanda ya jawo yaduwar akidar ta’addanci a tsakanin musulmin turai wadanda ake rudarsu ana wanke musu tunani.
3453831