IQNA

Daesh Ta Sanar Da Jerin Sunayen Biranan Da Za Su Kai Wa Hari A Nan Gaba

21:02 - November 23, 2015
Lambar Labari: 3456297
Bangaren kasa da kasa, jaridar International Business Times ta ta buga cewa yan ta’addan Daesh sun fitar da wani sabon jerin sunayen biranan da za su kaiwa hari.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, masu bata shafukan yanar gizo (Anynomos) sun gano sunayen biranan da Desh ke shirin kaiwa hari da suka hada da biranan Faransa, Indonesia, jahar Georgia da ke Amurka, Rom da Milan, da jami’ar Ruhul quds da ke kasar Lebanon.

Port Johnson jami’I na hukumar yan sanda mai bincike ta FBI ya sheda wa kamfanin dilalncin labaran Sporting na kasar Rasha cewa suna da bayani kan shirin kai hari a Georgia, amma bas u da cikakken bayani kan yadda lamarin yake ko kuma wani tabbataci daga wata majiya mai tushe.

Majami’ar Ruhul quds da ke kasar Lebanon ta dakatar da gudanar da tarukanta da ta shirya gudanarwa a gobe sakamakon wannan rahoto.

Wasu masu bin diddigin lamrra na yanar gizo sun shiga bincike kan harkokin kungiyar ta’addnci ta hanyar yanar gizo wadda ita ce hanyar da suke bi domin gudanar da ayyukansu.

Kungiyoyin da ke suke gudanar da wadannan ayyuka ta hanyar yanar gizo da aka bude tun a cikin shekara ta 2002 sun bayyana cewa sun sha lawashin daukar fansa kan kungiyoyin ‘yan ta’adda, tare gano sirrinsu da kuma fallasa su.

Anynomos sun sanar da shelanta yaki kan ‘yan ta’adda tun bayan kai harin birnin Paris.

3455860

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha