IQNA

Ta’addanci wata Cuta Ce da Ke Barazana Ga Dukkanin kasashen Duniya

19:40 - November 24, 2015
Lambar Labari: 3456736
Bangaren siyasa, Dr. Rouhani shugaban kasar Iran a lokacin da yake ganawa da shugaban Najeriya ya bayyana cewa kasashen biyu suna da abu guda da suke da mahanga guda akansa shi ne ta’addanci wanda ya kamata a hada kai domin a yake shi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shugban kasa cewa, Hojjatol Islam Hassan Rauhani shugaban kasar Iran a lokacin ganawa da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa kasashen biyu za su iya yin aiki tare a bangarori masu yawa.

Ya ci gaba da cewa daya daga cikin muhimman lamurra da suke daukar hankali a halin yanzu shi ne batun ta’addanci wanda ya adddabi duniya da al’ummominta, wanda kuma ko shkka babu lamari ne da kasashen biyu za su iya yin aiki tare domin fuskantarsa.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa kasarsa za ta yi aiki kafada da kafada tare da Iran a dukkanin bangarori, kasantuwar kasashen biyu na da kyakkyawar alaka a tsakaninsu wadda ta jima, kuma har yanzu bas u gushe a matsayinsu na aminan juna ba, musamman ma a kwai lamurra da dama da suka hada su.

Dr. Rouhani ya kara da cewa kasashen biyu suna da alaka a bangarori na kasuwanci da ilimi kamar yadda kuma suke a matsayin mambobin na kungiyoyin da ke sayar da man fetr na duniya haka nan kuma a bangaren skar gas.

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammad Buhari ya nuna gasuwarsa matuka dangane da yadda ziyarar ta kasance, inda y ace ko shakka babu Najeriya a shirye take ta ci gaba da kara fadada alakarta da Iran, musamman ganin cewa kasar Iran ta samu ci gaba a dukkanin fuskoki, musamman ma ta fuskar ayyukan mai da gas da kma karfin wutar lantarki.

3456583

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha