IQNA

Ayatul Kursiy Ita Ce Aya Mafi Girma A Cikin Kur’ani

21:17 - November 27, 2015
Lambar Labari: 3457476
Bangaren kasa da kasa, malamin shari’ar musulnci a jami’ar Azahar ya bayyana cewa ayatul kursiy it ace ayar da ta hada siffofin Jamaliyya, da kamaliyya, da jalaliyya na ubangiji.


Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albalad cewa, Ahmad Karima mamalin sharia a jami’ar Azahar ya bayyana zantawarsa da tashar Al-asimah cewa, ayatul kur’ay ta kunshi sunayen ubangiji masu girma, saboda haka ita aya mafi girma a cikin ayoyin kur’ani mai tsarki.

Karima ya ce lafazin (Allah) wanda ya zo daga farko wanann aya yana nuni da ubangiji madaukakin sarki kai tsaye, wanda shi ne mai wajbcin samuwa koma bayan dukkanin talikai.

Malamin ya kara da cewa, wasu malamai sun jaddada cewa sunan Alhayyu Alqayyum sunan ubangiji ne mafi girma, wanda ya zoa  cikin sunayen farko na ubnggiji a wannan aya mai albarka.

3457402

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha