Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Canoe» cewa, musulmi mazauna birnin Alborta na kasar Canada sun nuna rashin gamsuwarsu da matakan takurawa da cin zarafinsu da ake dauka.
Hakan kuwa ya zo ne sakamakon yadda a cikin loktannan wasu masu tsananin kiyayay da musulmi suke cin zarafinsu da suna yaki da ta’addanci, da hakan ya hada har da wasu daga cikin jami’an tsaron kasar masu kin addini.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin musulmin kasar Canada suna kokawa kan yanayin da suka tsinci akansu a ciki tun bayan harin da aka kai a kasar trai a kwanaki baya, wanda hakan ya bar mummunan tasiri kan lamarin.
Yanzu haka dai ana kira ga musulmin nahiyar turai da su zama cikin fadaka, domin akuce ma fadawa a cikin duk wani tarko da za iya dana musu.
3458751