Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «The Eagle Online» cewa, an gdanar da jerin gwanon a garin kaduna wanda ya kare a Husainiyar Baghiyyatollah a Zaria.
A makon da ya gabata an yi irin wanann jerin gwano wanda yan ta’addan Boko haram suka kaiwa hari, wanda kuma hakan ya yi sanadiyyar yin shahadar mutane 24 tare da jikkatar wasu.
Yuhana Buro shugaban mabiya addinin kirista a majami’ar Kaduna na daga cikin wadanda suka halarci wannan jerin gwano.
Wannan jerin gwano ya samu halartar musulmi dsaga koina a cikin Najeriya da suka hadu.
Harkar musulmincia Najeriya karkashin jagorancin sheikh Ibrahim Zakzaky ce ke gudanar da wannan taro kamar yadda aka saba.
3458941