IQNA

Taron karatun Kur’ani Na Kasa Da Kasa A Kasar Iraki

23:28 - December 07, 2015
Lambar Labari: 3460937
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da taron karatun kur’ani mai tsarki na kasa da kasa a Nasiriyyah da ke lardin Ziqar na Iraki tare da halartar makaranta daga kasashen duniya.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadsarwa na yanar gizo na QAF cewa, wannan taron karatun kur’ani zai samu halartar Ahmad Ahmad Nu’aina’a daga Masar, Sayyid Muhammad Jawad Hussaini, Sheikh Maisam Tammar daga kasar Iraki.

Wannan taron karatun kur’ani mai tsarki dai ana shirya shi tare da gudanar da shi ne a kowace shekara, wanda cibiyar Al-nukhba da ke lardin take nauyin shiryawa.

A wannan karon karon dai ana gudanar da wannan babban taron karatun kur’ani na kasa da kasa nre bisa taken raya a’adun muslunci, karkashin cibiyar Habibullah.

Daga ranar 15 ga watan Azar ne za a fara taron zuwa 21 ga wannan wata na Azar.

3460555

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha