IQNA

Minista Kirista A Masar Ya ce Zai Kare Martabar Musulunci

23:18 - December 08, 2015
Lambar Labari: 3461369
Bnagaren kasa da kasa, daya daga cikin ministocin kasar Masar kirista ya ce zai kae martabatar addinin muslunci a ciki da wajen kasar gwargwadon ikonsa.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-shuruq cewa, Nabila Mukrim Abdul shahid Minista mai kula da harkokin srawa mazauna kasashen ketare ya ce zai kare mutuncin muslunci a duk inda ya samu kansa.

Minsitan ya bayyana hakan ne sakamakon abubuwan da suke faruwa a kasar dama sauran kasashen duniya, inda ake tsangwamar muslunci da sunan ta’addanci, inda ya fahimci cewa ana zaluntar musulmi a kan wannan batu.

Daya daga cikin abin da ya kara jan hankalinsa shi ne yadda ya fahimci cewa abin da muslunci yake koyarwa daban a bin da kuma yan ta’adda suke da sunan adinin muslunci daban, kuma tuhumar musulmi da abin da abin da yan ta’adda suke yi ba adalci ba ne.

Tun bayan bullar kungiyoyin yan ta’adda a cikins hekarun wadanda kasashen turai da na larabawa suke daukar nauyin kafa su da kuma ba su horo na ayyukan ta’addanci a cikin kasashen musulmi, masu adawa da Musulunci sun yi amfani da wannan damar domin cin musutunci Musulunci.

Nabila Mukrim Abdl Shahid ya bayyan a taron ministocin kasar Masar cewa, ya zama wajibi a kara mayar da hankali wajen taimakon marassa galihu a kasar, tare da duba wasu daga cikin bukatunsu na gaggawa.

3461300

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha