Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, tsohon shugaban hukumar liken asirin Birtaniya MI6 ya tona asirin tsohon shugaban hukumar liken asirin Saudiyya Bandar Bin Sultan da ke sheda masa ta wayar tarho cewa za su kashe yan shia da alwiyyawa kamar yadda aka kashe yahudawa a Jamus.
Jaridar Indepent ta kasar Birtaniya ce ta buga labarin da ta nakalto daga Richard Dirlao cewa, tun kafin harin Satumba an shirya yin kisan kiyashi kan ‘yan shi’a da alawiyawa wanda gwamnatin Saudiyya ce ta shirya hakan.
Jami’in yace abin da yake faruwa a yanking abas ta tsakiya a halinyanzu an riga an shirya shi tsaf tun kafin ya faru, kuma kasashn larabwan yankin ne tare da hkumomin liken asiri na kasashen yamma suka shurya hakan, duk kuwa da cewa larabawan ke daukar nauyin lamarin da kudinsu.
Ya ce lokacin kisan yan shia da Bandar Bin Sultan ya sheda masa ya yi, domin kuwa tun daga shekara ta 2003 aka fara aiwatar da hakan bayan mamaye kasar Iraki, inda daga nan aka fara kashe yan shia ta hanyar kai musu harin kunar bakin wake da bam.
Daga cikin abubuwan da suke faruwa ahalin yanzu kuwa, har yadda kasashe irin su saudiyya suke daukar nauytin ‘yan ta’adda wadanda suka mamaye lardin Nainawa da kuma Mausil, da kisan kiyashin da ake yi way an shi’a na yanka su da ransu a gaban iyansu da danginsu, ana cin zarafin matansu, kamar yadda aka yi a shekara ta 1940 a kasar Jamus.
Jaridar ta ce a tabakin wannan babban jami’in liken asirin kasar Birtaniya kafa kungiyoyin yan ta’adda irin su Daesh da sauransu, yana daga cikin wannan shiri na kisan yan shi’a da Saudiyya ta shirya, wanda kuma an hada baki da wasu kasshen yankin domin aiwatar da shi, ta hanyar kungiyoyi irin su Taliban Alkaida, Lashgar Tayyibah a Pakistan da sauransu.
Jami’in ya ce dalilin sabanin alkaida da saudiyya shi ne harin da suka kai cikin kasar, alhali yarjejeniyarsu ita ce Alkaida ta kai hari a waje.
3461558