IQNA

Haramin Imam Ali (AS) Na Shirin Karbar Miliyoyin Masi Ziyara

23:48 - December 09, 2015
Lambar Labari: 3461863
Bangaren kasa da kasa, haramin Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf na shirin karbar miliyoyin masu gudanar da aikin bauta na ziyara domin tunawa da lokacin rasuwar manzon Allah (SAW)


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, a wani zama da aka gudanar a tsakanin jami’a masu kula da hubbaren Imam Ali (AS) sun bayyana cewa 28 ga watan Safar lokaci ne na ziyarar miliyoyin muminai, kma an shirya tarbarsu.

Wadanda suka halarci zaman sun bayyana gamsuwarsu da abubuwan da aka tttauna na daukar nauyin kla da baki masu ziyarea a wannan wurin mai tsarki.

Sayyid Nazzar Hablullah Matin daya daga cikin manyan shugabanni masu kula da harkokin hubbaren mai tsarki ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai sun kammala dukkanin shirin da ya kamata domin gudanar da wadannan taruka masu albarka.

A gobe Alhamis hutu a hukumance a birnin Najaf sakamakon tarukan ranar 28 ga watan na wafatin manzon Allah (SAW) wada miliyoyin muminai daga koina cikin kasar da ketare sukan zo domin ziyartar hubbaren Imam Ali (AS) da kuma raya wannan rana.

Muhammd Khazali babban jami’I mai kula d aharkokin hulda da jama’a da yada labarai da suka shafi hubbaren mai tsarki ya bayyana cewa, wannan yana daga cikin lokutan da birnin kan karbi baki daga koina da suke zuwa omin halartar tarukan da ake gudanarwa a wanan hubbare mai tsarki.

Abin tuni a nan dais hi ne a ranar Juma’a ne ake gudanar da hutu na wafatin manzon Allah, kasantuwar a ranar ya yi daidai da kwanan watan da kasar take bi.

3461690

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha