Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, Muhammad Ali tsohon fitaccen dan wasan dambe na duniya yay i kaakusar suka dangane da cin zarafin mulmi da kum kalaman batunci da Donald Trump ke yi a lokacin yakin eman zabe a cikin kasar, da nufin yin amfani da hakan wajen neman kuri’a.
Wannan suka ta tsohon dan wasan damben ta zo ne adaidai lokacin da kungiyoyin muulmin kasar Amurka da na wau kasashen duniya suke yin kakkausar suka kana bin da Trump yake yi, wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.
Muhammad Ali ya ce shi kansa musulmi ne, kuma wadanda suke aikata ta’addanci da sunan Musulunci hakika ba suna wakiltar musulmi ba ne balanta addinin muslunci wanda ke kira zuwa ga zaman lafiya da girmama dan adam.
Donald Trump ya zage wukarsa daga kube ne yana mai nunata a kan musulmi, adaidai lokacin da ayukan ta’addanci da kungiyoyin ‘yan ta’adda da wadada Amurka da kawayenta ne suka samar da su da nufin cimma wannan manufa ta bata sunan addini, suke zafafa hare-harensu na ta’addanci.
Daya daga cikin wuraren da ya yi yi suka akan musulmi shi ne jahar California inda aka kai harin ta’addanci a kan Amurkawa, wanda kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa ta sanar da cewa ita ce keda alhakin kai harin, amma Trump ya dora alhakin hakan kaco kaf a kan dukkanin musulmi.
Bisa ga wani rahoto na jaridar Hall an bayyana cewa yanzu haka dai Trump yana samun goyon bayan Amurkawa da dama inda wasu da aka ji ra’ayoyinsu kianin kashi 65 suka ce shi za su jefa ma kuri’arsu.
3461914