IQNA

An Kashe Yan Shi’a Da Dama Tare Da Jikkta Wasu A Najeriya

23:10 - December 13, 2015
Lambar Labari: 3462780
Bangaren kasa da kasa, hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Nigeriya suka kai kan gidan shugaban Harkar Musulunci a Nigeriya an asarar hasarar rayuka da na dukiyoyi.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Alalm cewa, harkar muslunci a Najeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta karyata bayanin da sojoji sika bayar da ke cewa sun kai hari kan babban hafsan hafsoshin sojin kasar a Zariya.



Shafin yanar gizo na Islamic Movement na harkar 'yan uwa musulmi ya karyata bayanin da sojojin suka bayar, da ke cewa 'yan uwa musulmi sun hana babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Burutai a lokacin da yake shirin wucewa ta wurin da suka kafa shingaye, inda bayanin ya ce taro ne za a gudanar na saka tuta a babban markazin husainiyya bBakiyyatullah da ke garin.



Amma tun kafin lokacin an jibge sojoji da makamai a wurin, daga bisani kuma suka kai farmaki tare da kashe wani adadi daga cikinsu.



Haka nan kuma shafin 'yan uwa musulmin ya karyata rahoton da wasu kafofin yada labarai na turai suka bayar da ke cewa babban hafsan hafsoshin sojin na Najeriya ya tsallake rijiya ta baya a Zariya, a lokacin da suka yi masa kwanton bauna.



Tun daga jiya Asabar ce sojojin gwamnatin Nigeriya suka fara farma magoya bayan Sheikh Yakub Ibrahim Zakzaki kan zargin tsare hanya a daidai lokacin da babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar ke shigewa a lokacin da magoya ke shirye-shiryen isa cibiyar gudanar da harkokin addini a garin Zariya da ke jihar Kaduna



Inda sojojin suka kashe mutane mutane da dama tare da jikkata wasu da dama, sannan a safiyar yau Lahadi sojojin kasar ta Nigeriya sun sake kai farmaki kan cibiyar gudanar da harkokin na addini.



An Kashe Mataimaki Da Kuma Likitan Sheikh Zakzaki



Rahotanni sun ce an kashe sheikh Mahmud Muhammad Turi mataimakin Sheikh Ibrahim Zakzaki, kamar yadda kuma aka kashe likitansa Musataf Saeed.



Har yanzu dai sojojin a cikin motocin yaki masu sulke suna ci gaba da killace unguwar da malamin yake, kamar yadda kuma aka tabbatar da cewa an kashe mutane da dama daga cikin magoya bayansa.



An yi amfani da manyan makamai da suka hada da bam da uran motoci tankokin yaki wajen rusa gidansa baki daya da ke wannan unguwa.



3462748







Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha