IQNA

Hare-Haren Sojojin Najeriya Kan Mabiya Mazhabar Shi’a

23:15 - December 13, 2015
Lambar Labari: 3462781
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane 7 aka tabbatar da cewa sun rasa ransu wasu da dama kuma suka ji rauni a harin da sojojin suka kai a kan yan shia a jiya da yamma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, sojojin Nigeria sun bude wuta kan Husainia Baqiyyatullah nay an shia almajiran Malam Ibrahim Zakzagi da ke Zaria a rewacin kasar a jiya Asabar.



Mai watsa shirye hsiryensa da harshen turanci a nan Tehran ta ce sojojin sun bada rahoton cewa yan shia almajiran Malam Ibrahim Elzakzaji sun tsare hanyar waucewar babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Lieutenant General Tukur Yusuf Buratai wanda yake ziyarar aiki a nan Zaria.



Sai dai majiyar harka Islamiyya wacce Malam Ibrahim Zakzaki yake jagoranta ta musanta hakan. A lokacinda ta yi hira ta wayar tarho da Nasir Tsafe Umar wanda ya ganewa idanunsa abinda ya faru ya ce sojoji ne suka fara bude wuta kan yan uwa wadanda suke cikin husainiyya Baqiyyatullah, ya kuma kara da cewa dama sojojin sun yi shirin hakan tun da dadewa.



Akalla mutane bakawai aka tabbatar da cewa sun rasa ransu wasu da dama kuma suka ji rauni a harin da sojojin suka kai a kan yan shia a jiya da yamma.

3462419

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha