IQNA

Kungiyar Hizbullah A Iraki Ta Yi Allawadai Da Kisan Shi’a A Najeriya

23:28 - December 14, 2015
Lambar Labari: 3463203
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hizbullah a Iraki Ta Yi Allawadai da kisan shi’a a Najeria da sojojin kasar suke yi babau kakkautawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ittijah Press cewa, an yi Allah dawa dai da ahari kan mabiya Ahlul bait (AS) a Najeroya daga sojojin kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar jamhuriyar muslunci ta kirayi mataimakin jakadar Nijeriya a Tehran don nuna damuwarta dangane da hare-haren da sojojin Nijeriyan suka kai wa shugaba da mabiya harkar Musulunci ta kasar tun daga ranar Asabar din da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewar da ranar yau Litinin ne ta kirayi mataimakin jakadan Nijeriya a Iran din don nuna damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abin da ke faruwa a Zariyan lamarin da yayi sanadiyyar kashewa da kuma raunana wani adadi mai yawa na 'yan kungiyar 'yan'uwa Musulunci na kasar karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Shi ma a nasa bangaren Magashin yayi alkawarin isar da wannan sakon ga mahukuntan kasar a Abuja.

Kafin haka ministan harkokin wajen kasar a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da takwararsa na Nijeriyan, a yau din nan ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta dau matakan da suka dace wajen kare lafiya da kuma ci gaba da zubar da jinin mabiya tafarkin Ahlulbaiti na Nijeriyan.

Wanann lamari dai bai dadi ga dukaknin mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo a kasar da ma sauran kasashen duniya ba, inda ake ci gaba da yin kira da a gaggauta sakin sa ba tare da bata lokaci ba.

3463049

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha