IQNA

Akwai Hannun Waje A Kisan Kiyashi Kan Yan shi’a A Najeriya / Da Nufin Hana Shi’anci yaduwa

23:21 - December 18, 2015
Lambar Labari: 3465575
Bangaren kasa da kasa, Ali Alali ya bayyana cewa akwai hannun kasashen ketare a harin da aka kai kan ‘yan shi’a a Najeriya da nufin hana mazhabar shi’a yaduwa a kasar baki daya.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya bayyana cewa a zantawa da Ali Alali marubuci dan kasar Kuwait  cewa akwai hannun kasashen ketare a harin da aka kai kan ‘yan shi’a a Najeriya da nufin hana mazhabar shi’a yaduwa a kasar a wannan lokaci.



A daya bangaren kungiyar kiristoci da Nigeria da kuma majalisar koli ta al-amuran musulmi a tarayyar Nigeria sun bukaci gwamnatin kasar ta gudanar da bicike kan kisan kiyashin da ya fari a birnin Zaria.



Kungiyar kiristoci da Nigeria da kuma majalisar koli ta al-amuran musulmi a tarayyar Nigeria sun bukaci gwamnatin kasar ta gudanar da bicike kan kisan kiyashin da ya fari a birnin Zaria.



Jaridar ta Nigeria ta nakalto masu magana da yawun kungiyoyin biyu wadanda suke magana a madadin musulmi da kiristocin Nigeria suna fadar haka. kakakin kungiyar  sake ya bukaci shugaba a kafa komitin don gano musabbabin kisan kiyashin da kuma daukar matakan hana faruwan hakan a nan gaba.



Har'ila yau ya musanta labran da tashar television ta mai watsa labaranta da harshen turanci a nan ta watsa na cewa kungiyar tana da hannu a cikin rikicin abinda ya faru Zaria.



A nata bangarem majalisar koli ta al-amuran musulmi ta kafa komitin mutane bakwai wanda ya kunshi manya manyan shuwagabannin kungiyoyin musulmi don sasanta bangarorin biyu.



Ya ce kungiyar tana bakincin abinda ya faru a zaria ta kuma yi kira da abi lamarin a hankali don tabbatar da zaman lafiya a kasar.



Kungiyoyin kare hakkokin bil'adama na kasa da kasa sun ci gaba da kiran da a gudanar da bincike mai zurfi dangane da rikicin da ya faru tsakanin jami'an sojin Nijeriya da 'yan kungiyar 'yan'uwa musulmi na kasar karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky don hukunta wadanda suke da hannu ciki.



A nata bangaren, kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Amnesty International, ta bakin shugabanta a Nijeriya, ta yi kiran da a gudanar da bincike mai zurfi don gano adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan yamutsin da kuma hukunta duk wani da ke da hannu cikin rikicin daga dukkan bangaren.



Ita kuwa kungiyar kare hakkokin bil'adama ta Musulunci da ke birnin Landan, ta bakin shugabanta, ta bukaci da a gudanar da bincike na kasa da kasa dangane da abin da ya faru a Zariya.



Har ila yau kungiyar ta yi kakkausar suka dangane da irin halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa suke nunawa abin da ya farun.



Rahotanni daga Nijeriyan suna nuni da cewa daruruwan 'yan kungiyar 'yan'uwa Musulmin ne sojojin suka kashe baya ga wadanda suka sami raunuka da kuma wadanda aka kama sakamakon wannan rikicin da sojojin suka zargi 'yan'uwa musulmin da kai musu hari lamarin da su kuma suka musanta.



3463823

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha