IQNA

An Zargi Radio Quran Na Masar Da Gaba Da Addinin Muslunci

22:51 - December 21, 2015
Lambar Labari: 3467971
Bangaren kasa da kasa, an zargi radio quran na kasar Masar da gaba da addinin muslunci sakamakon mara baya da yake yi ga sojojin kasar.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, ‘yan salafiyyah sun tuhumi radio quran na kasar Masar da gaba da addinin muslunci sakamakon mara baya da yake yi ga sojojin gwamnati a yakin da ske yi da yan ta’adda.

Muhammad Awidah shugaban radio kuran na kasar Masar ya bayyana cewa, an yi musu diorar mikiya saboda matsayar da suka dauka wajen ganin suna wayar da kan mutanen kasar domin a samu zaman lafiya da kuma kauce ma fadawa cikin ayyukan ta’addanci.

Ya ce wannan ya sanya bangarorin da suke yada akidar ta’addanci fusata da kuma yin dirar mikiya kan wannan gidan radio, har da bayyana shi a matayin wurin yada gaba da addinin muslunci.

Muhammad Awidah ya ci gaba da cewa ana zarginsu da mara ma sojoji baya kana bin da yake faruwa  akasar, alhali kuwa  acewarsa sub a su Magana kan duk wani abin da ya shafi siyasa ta kowane bangare, abin da suke mayar da hankalia  kansa shi ne batun gyara dabiun jama’a.

Haka nan kuma ya bayyana abin da suke da cewa wani aiki na wajibi domin yada kur’ani da koyarwarsa  akasar Masar, tare da wayar da kan matasa danganeda dabiun addinin msulunci wadanda kur’ani mai tsarki yake koyar da dana dam.

Kungiyar salafa a Masar da ke da alaika da kungiyoyin yan ta’adda na ciki da wajen kasar suna nuna damuwa kan wannan gidan gidan radio, domin bayan yada akidun ta’addanci da suka ginu kan koyarwar salafiyanci.

Khalid Said kakain kungiyar ya bayyana cewa wannan gidan radio yana bata sunan ma’aiki (SAW) a cikin shirinsa.

3467621

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha