IQNA

Azhar Na Shirin Karfafa Kasashe da Su Shiga Kawancen Saudiyya Domin Yaki Da Ta’addanci

23:18 - December 24, 2015
Lambar Labari: 3469044
Bangaren kasa da kasa, sheikhul Azhar baban malamin cibiyar a mako mai zuwa ne yake shirin kafa wani kawancen addinin somin mara baya ga kawancen Saudiyya da ake kira na yaki da ta’addanci.


Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iram News cewa, Ahmad Tayyib sheikhul Azhar a cikin mako mai zuwa ne yake shirin ganawa da wakilan kasashe 34 da aka gayyata cikin kawancen saudiyya, domin kafa wani kawancen addinin somin mara baya ga kawancen Saudiyya da ake kira na yaki da ta’addanci a cikin kasashen musulmi.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, ministan tsaron Saudiyyan ya sanar da kafa abin da ya kira 'hadakar kasashe 34 da nufin fada da ta'addanci' karkashin jagorancin kasar Saudiyya.

To sai dai kuma tun a lokacin, tun ma kafin wasu kasashen da aka sanya sunayen na su su fara nuna rashin amincewarsu, wasu suka fara sanya alamun tambaya kan manufar hadakar da kuma yiyuwar cimma nasararta, suna masu cewa wani irin hadaka ta kasashen musulmi ne za a kafa amma kuma wasu manyan kasashen musulmi, wadanda mafi yawansu ma suna fuskantar ta'addancin kai tsaye amma ba sa ciki.

Wani abin da ke kara sanya shakku cikin manufar Saudiyya kan kafa wannan hadakar shi ne cewa a daidai lokacin da Saudiyyan take sanar da kafa hadakar fada da ta'addancin, amma gwamnatocin kasashe wadanda suka zamanto tungar 'yan ta'addan a halin yanzu suna zargin kasar Saudiyya, tare da hadin gwiwan kasashe wadanda su ma suna cikin hadakar, a matsayin kasashen da suke kan gaba wajen goyon bayan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya musamman a kasashen Iraki da Siriya.

A saboda haka ne da dama daga cikin masana da masu fashin bakin magana suke ganin manufar kafa wannan hadakar karkashin jagorancin Saudiyya ita ce kokarin rarraba kan al'ummar yankin bisa tushen kabilanci da mazhaba da kuma rufe irin danyen aikin da Saudiyya take yi na kirkirowa da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Gabas ta tsakiya da ma sauran yankuna na duniya wadanda a halin yanzu suka fara zama karfen kafa hatta ga kasashen yammaci.

3468959

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha