IQNA

An Bijiro Da Batun sace Imam Musa Sadr A taron Makon Hadin Kai

13:54 - December 27, 2015
Lambar Labari: 3470007
Bangaren kasa da kasa, mamba kungiyar Amal ta kasar Lebanon ya bijiro da batun sace Imam Musa Sadr a taron makon hadin kai da aka bude a yau.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Al-diyar cewa, Khalil Hamdan mamba a kungiyar Amal,a  taron makon hadin kai da ke guda yanzu haka a birnin Tehran, ya bijiro da batun sace Imam Musa Sadr a taron.

Khalil Hamdan ya bayyana matsayin Imam Musa Sadr wajen kokarinsa na hada kan al’umma da kuma gwagwarmaya domin ganin cewa al’ummar msulmi ta samu yanci daga danniyar kasashe masu girman kai da yan koransu na yankin baki daya.

Inda kuma ya tabbatar da cewa har yanzun, bayan shekaru talatin da shida da bacewar Imam Musa Sadar da abokan tafiyarsa guda biyu, lamarinsu a raye yake a zukatan mutanen kasar.



Imam Musa Sadar ne ya kafa kungiyar ta Amal sannan  ya bace ne a kasar bya a shekara dubu da dari bakawai da sabain da takwas a wani ziyarar aiki da kai kasar, bisa gayyatar shugaban kasar .



Duk kokarin da aka yi na sanin halin da suke yake ciki tun lokacin, bai samu nasara ba.



3469878

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha